13 Satumba 2025 - 10:08
Source: ABNA24
Military Watch: Aljeriya Ita Ce Kawai Ƙasar Larabawa Da Ke Da Karfin Kare Hare-Haren Isra'ila

Hare-haren da Isra’ila ta kai kan Qatar a baya-bayan nan ya haifar da ayar tambaya game da yadda sojojin saman Isra’ila za su iya kutsawa cikin wasu kasashen Larabawa, da kuma karfin da wadannan kasashen ke da shi wajen dakile hare-hare.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: mujallar nazarin soja ta "Military Watch" ta rubuta cewa: Aljeriya tana da karfin kariya sosai daga duk wani harin da Isra'ila za ta iya kaiwa saboda ci gaban tsarin makaman da ta sayo daga Rasha da China. Sabanin haka, yawancin ƙasashen Larabawa suna ci gaba da dogaro da tsarin yammacin duniya tare da takaitacciyar fasaha kuma suna fuskantar matsananciyar matsalolin siyasa. Lambobin sirrin manhajojin wadannan makaman ma kasashen yamma a kayyade su ke, tare da hana amfani da su wajen sabawa muradun kasashen Yamma din. Wannan ya tabbatar da 'yancin daukar mataki ga kasashen Yamma da Isra'ila na kai hare-hare ta sama kan kasashen Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.

Mujallar ta bayyana cewa, duk da nasarar da Isra'ila ta samu wajen kai hare-hare da dama a yankin, da suka hada da Syria, Lebanon, Yemen da Qatar, karfin sojanta ya dogara ne kan raunin tsaron da makiyanta ke da shi fiye da karfin fasaharta.

Har yanzu dai jiragen saman Isra'ila sun dogara ne akan tsofaffin jiragen F-15 da F-16, wadanda ba su da sabbin na'urorin rada da na yakin zamani, yayin da adadin jiragen F-35 na zamani ke da iyaka.

A cikin wannan lamari, Aljeriya, ta na da matsayin keɓantacce na musamman a yankin, ta ɗauki dabarun tsaro mai zaman kanta tun farkon shekaru goma da suka gabata - musamman bayan faduwar gwamnatin Gaddafi a Libya a shekara ta 2011, wanda ya jefa ta ga mummunan rikicin tsaro da kuma nuna haɗarin dogara ga raunin kariya daga hare-haren sama daga waje.

Tun daga wannan lokacin, Aljeriya ta ba da gudummawa sosai wajen gina hadaddiyar cibiyar sadarwa ta tsaro ta sama, wacce aka sayo su daga Rasha da China: daga na'urorin radar zamani zuwa na'urorin makamai masu linzami masu cin dogon zango zuwa sama da kuma tarin jiragen yaki na zamani.

Kashin bayan tsaron saman Aljeriya ya kunshi tsare-tsare kamar haka:

Na’urorin makami mai linzami daga sama zuwa sama: S-300PMU-2, S-400 da HQ-9 na kasar Sin

Babban runbun kayan yakin Rasha da ke dauke da jirage nau’in Su-30MKA sama da 70

Jirgin Su-35 na zamani na Rasha jiragen yaki masu ci gaba

Na’urorin tsaron sama na matsakaicin zango irin su Buk-M2 na Rasha

Jiragen yaki nau’in MiG-29M na Rasha

Don haka wannan tsarin tsaro tana haifar da kalubale na musamman a yankin ga duk wani hari da Isra'ila ko kasashen yammacin Turai za su iya kaiwa. Idan aka yi la’akari da matsayinta, Aljeriya ta dogara ne da jiragen yakin da suka fi na takwarorinsu na Isra’ila ko Turkiyya na zamani shekaru da dama.

Your Comment

You are replying to: .
captcha